album cover
Mai Waka
49,576
Pop
Mai Waka was released on December 29, 2020 by Jita Record as a part of the album Mai Waka - Single
album cover
Release DateDecember 29, 2020
LabelJita Record
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM92

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Isah Jita
Ali Isah Jita
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Mai waƙa
Mai waƙa
Mai waƙa
Mai waƙa (Prince production)
[Verse 2]
Ga fatan mai waƙa
Ga lafazin mai waƙa
Ga zancen mai waƙa
Ga hujjar mai waƙa
[Verse 3]
Na faɗa na ƙara, wanda ya so ka ka so shi
Wanda ya ƙi ka ka kyale shi
Hassada babban ciwo a zuciyar mai ƙulla ta
[Verse 4]
Na gaba tuni ya yi gaba tuni ya yi gaba, haka Allah Ya hukunta
Ga zuma rumbun daɗi, maɗaciya ba mu kulata
Tsuntsu daga Allah ne, ɗaukakarsa a duba ta
Jirgin sama ya yi sama, kwanya an nuna ta
Sowa ta kaure gari, mai faɗa ya shelanta
[Verse 5]
Mai waƙa ne ke waƙa
Kun ji azancin mai waƙa
Ko ina sai mun leƙa
Da farin zare za mu yi saƙa
Saƙon nan sai mun miƙa
Da mu da kowa da alaƙa
[Verse 6]
Mai waƙa sai mai waƙa
Ga Ali Jita mai waƙa
Ina Nazifi mai waƙa
Da Naziru ma sarkin waƙa
Ummar namu yana waƙa
Adamu Zango mai waƙa
[Verse 7]
Ado Gwanja na waƙa
Da Usaini Danko na waƙa
Adamu Nagudu yana waƙa
Lilin Baba yana waƙa
Baban Chakwai mai waƙa
[Verse 8]
Da El'mu'azu yana waƙa
Breaker Hamisu na waƙa
Nura M Inuwa waƙa
Lalayyo Baban waƙa
Mahmud ko ya bar waƙa
[Verse 9]
Dukanmu kun ga mawaƙa ne
Kowa yana da masoya ne
Wasu burinsu su ɓace mu
Wai mu 'yan nanaye ne
In mu 'yan nanaye ne, to kai ɗin ɗan wane ne
Waƙa tai mana komai ne
Idan ka musa kuma ka gane
[Verse 10]
Wani aikinsa siyasa ce
Wani kuma shi Ɗan sanda ne
Wani mai tuƙin jirgin ne
Wani ko shi alƙali ne
Wani likitan dabbobi ne
Wani likitan na mutane ne
Wani shi mai koyarwa ne
Amma wani kuma mai koyo ne
[Verse 11]
Siyo ka siyar aikin wani ne
Amma wasu kuma dillalai ne
Wani mai kamun Kifi ne
Wannan kun ga mahauci ne
Haka Allah ke ikonsa
Mu kuma kun ga mawaƙa ne
[Verse 12]
Hassada babbar cuta, Annabi ma yayi haninta
Kowa na harkarsa, ta mu wasu na damunta
[Verse 13]
Mai waƙa, ga zakin waƙa
Mai waƙa, ga Jitan waƙa
Mai waƙa, ga zakin waƙa
Mai waƙa, ga Jitan waƙa
Mai waƙa, ga zakin waƙa
[Verse 14]
Ga Jitan waƙa
Ga zakin waƙa
Ga Jitan waƙa
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...