Featured In

Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Ali Jita
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Amarya share hawaye bar kuka
Amarya ga kidanki kin farka
[Verse 2]
Kin ga aure shi ya sa ki kin girma
Arziki ne a duniya ake nema
In da kauna zaman gidanki ba fama
Addu'ata Allah ya kare 'yan gulma
[Verse 3]
Babu wai wai mijinki ga shi mai girma
So da kauna shi ya sa da alfarma
Shi yana sonki kin aminta ai kema
Shimfidar fuska ta wuce ta tabarma
[Verse 4]
Sannu Amarya gidan miji akwai dadi
Kin ga amarya a zantukanmu ba kaudi
Kin ji amarya kar batunmu yai fadi
Kar ki damu babu sidi ba sidi
Babu karya cikin gyada akwai gardi
Mai misali kantu yake kira ridi
[Verse 5]
Na ji labari a baya an ka sha fama
Da magauta da tsugudidi 'yan gulma
Kwanci tashi sun sallama a yau su ma
Rayuwa ce haka duniya ake fama
[Verse 6]
In fada ne nasara tana wajen kurma
An yi auren magauta sun sani su ma
Har wa'yansun su sun shigo bikin su ma
[Verse 7]
Ga ido fes a zuciya suna kuka
Ba kamanni farin suga cikin laka
Ga hakora ga zuciya tana tuka
Yanzu an kammale ginin ana jinka
[Verse 8]
Amarya, amarya lokaci ya yi
Ke amarya, amarya zamani ya yi
[Verse 9]
Mu muna dariya wadansu na kuka
Mun bi Allah su sun biyewa 'yan girka
Addu'armu muke su suna biye boka
[Verse 10]
Lokaci ne kowa da lokacinsa
Zamani ne, kowa da zamaninsa
[Verse 11]
Ai kamar wane kun ga ba ta wane
Mai abin ban biki ya je biki ne
Mai karatu ganinmu malami ne
Mai kwatance ganinmu dan gari ne
[Verse 12]
Da kun ga kura zuwa na ayari ne
To arziki dai ashe jinin jiki ne
Kuma mijinki mun gane jarumi ne
So da kauna sanadin farin zama ne
[Verse 13]
Sannu amarya, amarsu lokaci ya yi
Sannu amarya, amarsu zamani ya yi
[Verse 14]
Dena kuka mijinki ba rago ba
Kuma ba zai karya dukka alkawal ba
Kuma ba zai sha idan ba za ki sha ba
[Verse 15]
Kuma ba zai bacci in idonki biyu ba
Kuma ba zai kwana inda babu ke ba
Yace ba zai kara miki kishiya ba
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out