Music Video

Adam A. Zango - Gambara (official video)
Watch Adam A. Zango - Gambara (official video) on YouTube

Featured In

Credits

PERFORMING ARTISTS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Songwriter

Lyrics

Tsumagiya
Gumbar dutse igiyar ruwa mai tsarse
Ragayar dutse ajalin mai daki sai jigo
Toh, toh, toh
Dan Adam mai chanza hali nasa
Na sama ke take na karkasa
Babu imani a zuciyar yanzu kowa tasa yake tasa
Ehh kunji Adam Zango (hmm)
Zantuka zai irgo (hmm)
Ku saurara kuji zancensa abunda Zango ya hango ki
Ehh nafada nakara Ddan adam baya tsoron Allah (hmm)
Sannan acikin su kalilan wasu ke aikin Allah (hmm)
Wasu sun samu duniya sunata diban daula (hmm)
Wasu ko basuda komai kullum idonsu da kwalla
Mu taimaka dan Allah (wayyo)
Mu so juna da amana (hmm)
Sannan mu zauna lafiya (ha)
Mu chanza halayan mu saboda rayuwar ga bata da tabbas
Ehhh, gumbar dutse igiyar ruwa mai tsarse
Ragayar dutse ajalin mai daki sai jigo
Ehemm malam Adam Zango ga tambaya zanyi maka
Rayuwa da akwai matsala da mai da mai fa ka fuskanta
Kai, El Mua'az bari zancen nan
Rayuwar mu akwai muni
Kowa duk ya juye
Hausawa sun juye, yara ma duka sun juye
Kaga 'ya ta bunkasa, ba aure sai dai yawo
Dakata malam Zango ai laifin na samari ne
A'a, a'a na iyayene
Wasu sai kaga sun bar 'ya'ya nata daukar nauyin su
Toh hakan wai baiwa ce?
Kai, El Mua'az wace baiwace zakaga yarka Cikin daula
Bakasan sana'ar taba ma zakaga wai tasai hala
Rayuwa sai lahaula
Adamu Zango akwai ila?
Ehh tabbas fa akwai natsala
Burin kowa dai daula
Gumbar dutse igiyar ruwa mai tsarse
Ragayar dutse ajalin mai daki sai jigo
Iyaye dole kuyo tsari ku dinga bincika 'ya'yanku
Kuyo tarbiyar 'ya'yaku, wa inda Allah ya baku
Ku kaunace 'ya'yanku sai Allah yaji tausanku
Yarima fa dan Zango
Wasu sunce ka kaufsa wai dan ka fade halinsu
Kai kyalesu da shirmen su
Dama kowa yasan su
Mai san yaji sunansu
Yabini zan zazzano su
A'a Zango da ka barsu
Dan nima ai nasan su
Zango mai zamani
Yakaga wannan zamani?
El Muaaz da ka barni halayen fa akwai muni
An yarda akwai kaddara da tazo sai fa ace Allah
Gidan ka daya kone (kaji ance yin haka sai allah)
Motarka da an sace (kaji ance yin haka sai allah)
Ga wani ya rasa matarsa
Ga wani ya rasa 'ya'yan sa (sai a gaya maka yin haka sai Allah)
Gumbar dutse igiyar ruwa mai tsarse
Ragayar dutse ajalin mai daki sai jigo
Malam Adam Zango wai ya zancen Naira?
To in kayi kudi yanzu ba'a gaya maka sai Allah
Sai ace ai mun sanshi da chan bashida ko sisi
Daga yabi su lasisi
Abuja kila su kai pisi
Ko jini ko kan yaro ko kuma anbi ta bayan shi
Kaji sun manta akwai Allah da yayai talauci yayai daula
Ehh kunji Adam Zango (hmm)
Zantuka zai irgo (hmm)
Ku saurara kuji zancensa abunda Zango ya hango
Ehhh, kaga zancen addini abin ya chanza kalar launi
Bahaushe ya dauka cewa shine mai addini
A'a wanda duk koh ya dau Allah
Da Muhammadu manzan sa
Toh musuluncine tsani
Idan Inyamuri na sallah (kaji ance wai tubabbene)
Katafawa na Sallah (sai kaji ance tubane)
Idan Igala yace Allah (sai kaji ance sabon tuba ne)
In kaga dan Tubi na sallah (shima sai kaji tubane)
Ehh to ku sani a gurin Allah, dukkanin ku musulmaine
Yan uwan kuma juna ne, kuri'aninmu guda dayane
Ehh kunji Adam Zango (hmm)
Zantuka zai irgo (hmm)
Ku saurara kuji zancensa abunda Zango ya hango
Gumbar dutse igiyar ruwa mai tsarse
Ragayar dutse ajalin mai daki sai jigo
Adamu ya maganan waka dan wasu sunce shirme ce
Kai waka ai baiwa ce
In ka iyata ko ka dace
Dan jihili baya waka
Wasu sunce laifin ce
Da kafarata fa ka kauce
Kai kyale duka sun zauce
Sana'ar waka ilimice
In ka tsaftace har harshenka ka gyra tunani ka dace
Nagane tunanin ka Zango nima na auna
Ai ko wacce irin sana'a zaka samu wutarka da aljanna
Gatan Zango Waka
Ilimin Zango Waka
A cikinta ko nayi jari
Kuma bana in kari
Kai gorin ilimin boko Zango nikuma Zango akwai jari
Sana'a ta ga tsari
Ehh nayo ilimin bokon karshe wakace kai kuji Allah mai kairi
Ehh Zango dodon waka mai zakace wa abokanka?
Allah shi muku albarka
Mai barci kuma ya farka
In munyi ilimin bokon sana'ar hannu mu dan kama
Wani walda ya kama
Wadansu suje suyi kafinta
Wasu na gyran fanfo
Wadansu na aikin tuki
Wasu yan fim ne malam
Wadan su na harkan waka
Wani ba daukar hoto
Wadan su na turin baro
Wanda duk ya rike sana'a Allah kai masa albarka
Dan watarana ya zam zaki
Nan shine karshen wakar
Sa ido, sana'ar banza
Written by: Adam. A. Zango
instagramSharePathic_arrow_out