Top Songs By Sadiq Saleh
Similar Songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Sadiq Saleh
Songwriter
Lyrics
[Verse 1]
Kin ji cikon burina
Taho gefena
In ki ka bar ɓarina
Tabbas zai mi ni ɓarna
Sha kurumin ka rabina
Ba waninka a raina
In dai da ranka da raina
Za ka zamo angona
[Verse 2]
Ba zan rayu ba
Idan babu ke
Ki zauna da ni
Cikin duniya
Ni ma idan babu kai
Ba zan rayu ba
Zan zauna da kai
Cikin duniya
[Chorus]
Idan babu (Kai)
Idan babu (Ni)
Ta ya za ta yi daɗi zaman dauniya?
[Verse 3]
Akwai daɗi samun ɗiyar kirki
Da kalmomi na yau na same ki
Ki ban dama na samu yardarki
Cikin zuci na liƙa hotonki
Bakina bai wuce furta sunanki
A fagen so zan zama hadimi gunki
[Chorus]
Idan babu ke
Babu ni
Ta ya zan ji daɗin zaman duniya?
[Verse 4]
Wa ke ta samari kai ɗaya ne na saka a gabana
Kuma ka zama jari a cikin so samun ribana
Na sanya maɗauri na ɗaure ka cikin ƙalbina
Zo ga wani sirri na san za ka riƙe shi amana
Fatan alkhairi an yi min na samu rabona
Zan alfahari da kiran ka uba a gurin ʼya'yana
[Bridge]
Ba zan rayu ba
Idan babu kai
[Verse 5]
Ba ni idan ya zama ke ma ba kya nan
Ko damuwa nake idan kin zo shi kenan
Kai ne mafari sannan ƙarshen-ƙarshen nan
Tabbas a zuciyata ba ka da tsara nan
In kin furta mi ni
Kar ki ɓoye mi ni
Kai ma ka sani
Son ka na yi adani
Ni dai kawai ni girma lardin soyayya
Komai kake biɗa zan yi ma ka na shirya
Tsarinmu ni da ke har abadan abadiyya
Mun sha tabara ba mai toshe mana hanya
Written by: Sadiq Saleh