Featured In

Lyrics

Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Allah zansa a farko
Allah zansa a farko kan in fara bayani (Kuyi hakuri)
Ko ba komai kunsan shine wanda ya yoni (Kuyi hakuri)
Ya azurya ni da lafiya kun ganta gareni (Kuyi hakuri)
Kuma yai mani maganin komai dazai dameni (Kuyi hakuri)
Baiwa ya bani (Kuyi hakuri)
Ita kasa aka so ni(Kuyi hakuri)
Shine ya 'dagani duniya yau ta kalleni (Kuyi hakuri)
Banayin raini (Kuyi hakuri)
Kan wanda yafini (Kuyi hakuri)
Ƴan uwa ku biyoni (Kuyi hakuri)
Kuji abinda nakeyi (Kuyi hakuri)
Inda kuka ganni ba komai ya kaini wajen ba sai hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Duniya ce makaranta in ka ganka cikinta
Wani dadi wani ko wahala zaisha a cikin ta
Wani Sa zai kada wani sai ya kaiga farauta
Wani dai-dai zobo wani sai ya 'daga Fanta
Wani in ya huta
Wani sai ya wahalta
Wani baida gadon da zayasa kuncinsa ya kwanta
Wani ya sayi mota tafiyar 'kasa na saka kanta
Duniya a hakan a tare mu kwana mu tashi cikinta
Idan mun banbanta
Kar muyi 'kasaita
Mun rayu ayau wata 'kila gobe muna cikin 'kabari
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Haka zam mai godiya duk inda ka tsinci kanka (Kuyi hakuri)
In kana kukan rashi akwaisu dubu sun fika (Kuyi hakuri)
Kabar hangen sama tinda akwai na 'kasanka (Kuyi hakuri)
Nemo mai albarka
In kabi dole a bika (Kuyi hakuri)
Samu da rashi in kabi Allah zai baka (Kuyi hakuri)
Kazamo na gari in kafadi kowa zaijika (Kuyi hakuri)
Alkairin naka shi zai bika a bayan raanka (Kuyi hakuri)
Malaman mu ku 'dauka (Kuyi hakuri)
Shuwagabanni dukka (Kuyi hakuri)
Sarakuna san barka (Kuyi hakuri)
Yan 'kasa kuji dukka (Kuyi hakuri)
Komai yai zafi magani nai Allah ne kuyi nazari
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Kuyi hakuri
Ina rokon ku, in an 'bata maku Kuyi hakuri (Kuyi hakuri)
In anzageku ba yanka a jikinku (Kuyi hakuri)
An 'dauki hakkin ku Allah zai saka maku (Kuyi hakuri)
Yana bayanku al-'kawari yayo a gareku (Kuyi hakuri)
Ko cikin soyayya saurayi da budurwa (Kuyi hakuri)
In kunyi auren sunna mata da miji kuyi duba
Acikinta sana'a yau da gobe na dosheku
Duniya labari (Kuyi hakuri)
Harshena jari (Kuyi hakuri)
Na zubo alkairi
Furuci kan tsari (Kuyi hakuri)
Rokon ka nakeyi har kullum Allah ka dada man hakuri
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out