Featured In

Lyrics

Hubbi-hubbi
Hubbi-hubbi lai
Hubbi-hubbi lai
Ga hubbi-hubbi
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata ke ta bugawa
Nasan da son ki a raina
Tausaya mini karda na koka
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata kai tai duba
Nasan da son ka a raina
Alkawar bazan manta ba
Rabuwa da masoyi zafi
Ban zaton za muyi gamo ba (gamo ba, gamo ba)
Shekaru da yawa sun shude
Ban ganin ki bare nayi duba (nayi duba, nayi duba)
Yau na gan ki kamar a mafarki
Zuciyata banyi zato ba
Agaza mini kiyi mini rana
Zuciya tabar yin kuna
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata kai tai duba
Nasan da son ka a raina
Alkawar bazan manta ba
Ai batun nan naga misulci
Wanda ke sona zanyi dashi
Tun ada so na kamu dashi
Zuciya don har tayi dashi
In batu na ka yarda dashi
Amshi zoben so lura dashi
Koda yaushe kai nayi dubi
Da son ka rai na ke kwana
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata ke ta bugawa
Nasan da son ki a raina
Tausaya mini karda na koka
Hakuri iske wa muradi
Nesa yau ta zama kusanci (kusanci, kusanci)
Da ina faman yin kuka
Rashin ki na fada a maraici (maraici, maraici)
Yanzu munyi gamo nayi murna
Zuciya ta daina kadaici
Sahiba ki kusanta gare ni
Muyi zaman so tare da juna
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata kai tai duba
Nasan da son ka a raina
Alkawar bazan manta ba
Rabuwar da mukayi sanadi ne
Wanda ba'a sa mishi rana
Na dade a cikin wani hali
Don rashin ka abin dumfana
Yanzu nima na cika buri
Ganin ka yau da nake a gaba na
Zaman kadaici yau ya kare
Dani da kai yau ba bankwana
Hubbi-hubbi kauna
Zuciyata ke ta bugawa
Nasan da son ki a raina
Tausaya mini karda na koka
Mu gode Allah wanda yayi mu
Yasa muke soyayyar juna
Yasa amana tamu ta daure
Zaman da mun kayi babu hiyana
Hailala muyi istigfari
Muyo salatin da ga Amina
اللهم صل على مُحمد
Hamidun hadi bn Abdullah
Hamidun, Mahamudin
Mustapha daha Rasulullah
instagramSharePathic_arrow_out