Dari
COMPOSITION & LYRICS
Mashkur Umar
Songwriter
Lirik
Ina jin dadi
Eh ina jin dadi
(Sonane fah)
Ina jin dadin so
Ina jin dadi
Nima ina jin dadin so
Ina jin dadi
Ina jin dadin so
Ta nai min dadi
Idan na same ki a so bai zama nayi laifi ba
Ina jin dadin so
Ta nai mini dadi
Idan na same ka a so bai zama nayi laifi ba
Ko zani da nisa, bazan je bake ba
Bakya da makusa, ya so bazan yi dake ba?
Jinin mu gamo yayi, so bai kauce rabo ba
Gasan mu dake yayi nisa bai dashe ba
Yau dani ake soyayya banyi rako ba
Na kamu da so ina da dalili na bana shiriri ta ba
Ina a ciki can cikin so ban zama daban baya ba
Kana darasi kayi bayani yaya bazan karu ba
A barni da kai na yarda bazan tarayya da wani ba
Zo kalli jiki na so bai sa nayi rama ba
Mai son ya raba mu da kai baza nayi masa kara ba
Da kai nafi tunkawo yaya bazan jajirce ba
Nayi ciwo na kwanta nasan zaki ban magani
Laifi in nama zaka yafe nasan zaka min lamuni
Nasan zaki kare mutunci na in anyi min razini
Nima zaka kare mutunci in kayi haka kayi rawar gani
Da akwai magana a cikin zuciya ta, na dade ina sunsuni
Nima na dade ina so na furta kunya ce bata barni ba
In mun cire son zuciya
Zamu zauna lafiya
Sannan mu hada da hakuri
A gefe mu dauko dauriya
Toh kin ji ki bi a sannu
Kaima kaji ka bi a sannu
Ni mai daura ki a hanya ne
Ba mai cutar dake ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com