Top Songs By Hamisu Breaker
Similar Songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
Songwriter
Lyrics
Ba tambaya ba
Beats Amjad Records
Duba ki ga yanda sonki yai mini
Duk da na san ki na sane
Ki kalli cikin idanuwa na
Na san za su zayyane
Wannan al'ajab na so ne da kauna
Aikina kiranki ne
Da na faɗa ki ji
Ki bani agaji
In daina rangaji
Ki ɗan yi tsokaci
Ki ba ni maʼaji
Ba zancen na gaji
Ki kau da kuduji
A so ba ya ji
Labarin zuciya
Ni zaki tambaya
Abin da naka ji ya zarce duniya
Idan na waiwaya
Ko ko na sunkuya
Amsar guda nake ji kin zamon habibiya
Da sonki na banu
A kanki na sanu
Abin da ba ki sone ce in bar shi na hanu
Da sirri zai ganu
Ki damƙan a hanu
Shi zai fi min yawan sauƙi in bar maganganu
Ki zo ki dab dani
So zai min lahani
Ki tausaya wa ruhina ki ce ki nai da ni
Bana ji ban gani
Wa zai kula dani
Idan ya zama saɓaninki to a bar ni ni
Ina ƙulafuci
Sai kin ci za na ci
Har wanda za na ci ki ci tun da babu rikici
Ya za a yi in burge wacce nake so da ƙauna
Ya za a yi
Kalamaina sun kaɗanta, fahimceni sannan bi hanya
Kalamaina sun kaɗanta, fahimceni sannan bi hanya
Don na so tasoni ne ba guru babu laya
Babu ɗage babu ƙarya ni bani son riya
Ba don kwalliya ba, kuma ba don dukiya ba
Ba don zantuka ba, kullum ta yi min maraba
Ina son ki
Ina son ki
Ina son ki
Ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba
Ina sonki
Ina sonki
Ina sonki
Ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba
Ina sonki so na gaske ba yaudara ba
Midget Mix
Beats Amjad Records
Written by: hamisu said yusuf