Top Songs By Hamisu Breaker
Similar Songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
hamisu said yusuf
Songwriter
Lyrics
Beat Amjad record
Hayya ki kula min ki rufa min gode miki
Kataho min cire min dukan shamaki
Ki aza min rika min mu tare farmaki
Ka rubanya mu idaya muga yaya yake
Sai ki sanya wa gamanya saka sako take
Sakar sanka ta sirkeni sikewa nake
Saka sakon ki a hanunki ki miko
Daga kallonka nake sonka da baiko
Zo ki zauna dani
Ka zaman magani
Tausaya dan Allah ki tausaya min
Agaza dan allah ka agaza min
Ehh sanki shine dutsen fashin tama mai kwari
Zana furta akanki babu mai mun kure
Na kasance dominki bani son in kari
In akwai ki agu bazanga mata bah
Lafiya lau zauna abinka mai kaunata
Bani boye kaunarka ta taba min hanta
Shinfida nai wa zuciyarka za nai gata
Gun biddarka bazan hada da guraye ba
Manta kaina nake idan kina gu nima
Ga dabara idan na barki za nai fama
Tausaya min dari kawai yake sa kerma
Dan halali bazaya so sakin haure ba
Ya tabara ka bani jarumi kyawawa
Mai farar zuciya bi'amana son kowa
Wanda ke sona da gaskiya kamar dan baiwa
Koda muni bazana rasa mai sona ba
Ni kawai na aminta ikirari na ke
Koh makaho ne so a zuci nace sai ke
Cutukana idan dake kawai na warke
Duk jawabin bazai wuce ki ban yarda ba
Na zaga zauna ki tini tantabara karshen kauna
So bai jure rini yayi kaman zanen zabo
Tinanin da nake
Na zaga zauna ka tini tantabara karshen kauna
So bai jure rini yayi kaman zanen zabo
Tinanin da nake
In na fada yake sukana
Dama fura kiban dan kauna
Tinda abin yana damuna
Kar a raba zanji jiki
Zama namu dake
Gara ace kana gefena
Sai ka hado cikon burina
Tini kasan dukan sirrina
Maza ka fadan naka naji
A kalbinka sake
Midget mix
Written by: hamisu said yusuf